Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan

Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa yanzu na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga birnin Landan, kasar Birtaniya.

Bisa ga sanarwan fadar shugaban kasa mislain karfe 7:18 na daren nan, shugaba Buhari ya iso Najeriya bayan ya tafi kasar Ingila ranan 7 ga watan Mayu, 2018 domin ganawa da likitansa a birnin Landan.

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa shugaban kasan zai dawo ranan gobe Asabar amma Allah ya yi ya dawo yau Juma'a.

Wannan tafiya na gaggawa da shugaba Buhari yayi ya tayar da jijiyan wuya yayinda wasu yan kungiyar adawa sun yi kira ga shugaban kasa yayi murabus tun da bai da isasshen koshin lafiya.

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan

Wasu kuma sun ce zai fi alkhairi ga Buhari da kasa ga baki daya idan ya ajiye niyyar takara a 2019 domin kulawa da kiwon lafiyansa. Amma fadar shugaban kasa ta caccaki masu wadannan maganganu.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaban Buhari zai baro kasar Birtaniya da yammacin yau Juma;a, 11 ga watan Mayu, 2018 bayan ya je ganawa da likitansa.

KU KARANTA: Shekaru 5 uwargidata ta hana ni saduwa da ita, amma tana rabawa mambobin coci kyauta – Fasto

Legit.ng ta samo wannan rahoto ne daga jam'iyyar APC reshen kasar Ingila yayinda suka kai masa shugaba Buhari ziyara a gidan gwamnati dake Ingila.

Jawabinsu yace: "Mun kaiwa shugaba Buhari ziyara gabanin dawowarshi Najeriya da ranan nan"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel