Sabuwar bullar Ebola a Afirka: Hukumar WHO ta fara gangamin shiri kar cutar ta balle

Sabuwar bullar Ebola a Afirka: Hukumar WHO ta fara gangamin shiri kar cutar ta balle

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) tana shirye-shiryen magance mummunar cutar nan data damu al'ummar yankin Afirka wato Ebola, wadda ta bulla a wani yanki na kasar Congo, inda a yanzu haka ta fara yaduwa zuwa wasu garuruwa a yankin kasar

Sabuwar bullar Ebola a Afirka: Hukumar WHO ta fara gangamin shiri kar cutar ta balle

Sabuwar bullar Ebola a Afirka: Hukumar WHO ta fara gangamin shiri kar cutar ta balle

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) tana shirye-shiryen magance mummunar cutar nan data damu al'ummar yankin Afirka wato Ebola, wadda ta bulla a wani yanki na kasar Congo, inda a yanzu haka ta fara yaduwa zuwa wasu garuruwa a yankin kasar.

DUBA WANNAN: Banbanci tsakanin gurguzu da jari hujja a tattalin arziki da gwamnatanci

A ranar juma'ar din nan ne Mataimakin Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya a bangaren kai taimakon gaggawa, Peter Salama, ya bayyana cewa yana fatan kasar Congo zata bada damar aiwatar da gwaje - gwajen magungunan cutar, sai dai kuma ya gargadi cewar kwayoyin maganin suna da wuyar lamari. Ya ce hukumar lafiya ta duniya ta sanar da kasashe tara wadanda suke makwabataka da kasar ta Congo game da cutar, sai dai a halin yanzu ana ganin cewa akwai hadari ga yaduwar cutar cikin al'umma.

Allurar dai wadda hukumar lafiya ta duniya ta kaddamar, ta kirata da suna "rVSV-ZEBOV".

Hukumar tace a yanzu haka mutane 17 sun mutu tun lokacin da mazauna kauyen suka sanar da bullar cutar a watan Disamba.

Wannan shine karo na tara da aka rubuta rahoton bullar cutar a kasar ta Congo, tun lokacin da cutar ta fara bayyana a karon farko a shekarar 1970.

"Daya daga cikin alamun daya nuna cewar cutar Ebola dince shine ganin yanda wasu ma'aikatan lafiya guda uku suka kamu da cutar," inji Ministan lafiya Oly Ilunga a cikin wata sanarwa. "Halin da muke ciki yana damun mu kwarai da gaske, kuma muna bukatar taimakon gaggawa."

Wani mai magana da yawun darakta na hukumar binciken cututtuka na kasar ta Congo, ya ce masana daga bangaren gwamnatin kasar zasu zauna a ranar Alhamis din nan mai zuwa domin tattaunawa dangane da hanyoyin da zasu hana cutar ketare iyakar kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel