Bata lokaci a kaddamar da kasafin kudin Najeriya zai kawo wani cigaba da gyare-gyare a kasar – Ministar Buhari

Bata lokaci a kaddamar da kasafin kudin Najeriya zai kawo wani cigaba da gyare-gyare a kasar – Ministar Buhari

- Ministar kudade Mrs kemi Adeosun tace bata lokaci a sanya hannu a kasafin kudin najeriya na 2018 zai kawo wani cigaba a kasar da gyare-gyare

- Ministar tace dalili kuwa shine saboda kudaden kayayyaki na kasuwa sun canza kudi sannan kuma yanayin samun kudi a kasuwar ma ya canza shima

- Adeosun tace gwamnatin tarayyar zatayi okarin ganin ta rufe gibin da aka samu sakamakon bata lokacin da akayi wurin kasddamar da kasafin kudin

Ministan kudade Mrs kemi Adeosun tace bata lokaci a sanya hannu a kasafin kudin najeriya na 2018 zai kawo wani cigaba a kasar da gyaregyare.

Ministar a ranar Juma’a a birnin tarayya, tace dalili kuwa shine saboda kudaden kayayyaki na kasuwa sun canza kudi sannan kuma yanayin samun kudi a kasuwar ma ya canza shima.

Bata lokaci a kaddamar da kasafin kudin Najeriya zai kawo wani cigaba da gyare-gyare a kasar – Ministar Buhari

Bata lokaci a kaddamar da kasafin kudin Najeriya zai kawo wani cigaba da gyare-gyare a kasar – Ministar Buhari

Adeosun tace gwamnatin tarayyar zatayi okarin ganin ta rufe gibin da aka samu sakamakon bata lokacin da akayi wurin kasddamar da kasafin kudin.

KU KARANTA KUMA: Sufeto janar na yan sanda ya bukaci ‘Yan Najeriya da su marawa Buhari baya game da yaki da rashawa

Ministar tace tana da yakinin cewa za’a kaddamar da kasafin kudin na shekarar 2018, nan bada jimawa ba.

A halin da ake ciki, Shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris, yayi kira ga ‘Yan Najeriya dasu taya Buhari yaki da rashawa don dawo da martabar kasar kamar yadda take a shekarun baya.

Idris yayi kiran ne wurin liyafar da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta shirya na jami’an Superitendant Course (7) 2017/2018, a makarantar Sojoji dake jihar Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel