Ku tashi ku yaki cin hanci da kanku - IGP ga talakawa

Ku tashi ku yaki cin hanci da kanku - IGP ga talakawa

- Yayi kira ga jama'a da su marawa shugaba Buhari baya

- Watakil wasu masu adawa dashi su dauka ya koma siyasa da bambadanci ne

- A kwanakin nan wasu bangarorin gwamnati sun sako shi gaba

Ku tashi ku yaki cin hanci da kanku - IGP ga talakawa

Ku tashi ku yaki cin hanci da kanku - IGP ga talakawa

Babban Sufeton 'yan sanda na Najeriya IGP. Ibrahim Idris yayi kira ga al'ummar Najeriya da su bawa shugaba Muhammadu Buhari goyon bayan akan kudurin sa na yaki da cin hanci da rashawa, domin hakan ita ce hanya daya da zata dawo da martabar kasar.

Shugaban hukumar 'yan sandan yayi kiran ne a wurin wani taro da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tsara a makarantar horon sojoji dake jihar Kaduna wato (Nigerian Defence Academy, NDA).

Shugaban yace duk nasarorin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa take samu akan kwato kudaden da wasu masu sun zuciya suka sace a kasar nan, hakan ya faru ne saboda irin goyon bayan da shugaba Muhammadu Buhari yake bawa shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

"Inda badan goyon bayan da shugaba Muhammadu Buhari yake bawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa, da baza su samu da yawa daga cikin nasarorin da suka samu yanzu ba."

Shugaba Buhari baya son cin hanci da rashawa ko kadan, saboda haka ina kira ga al'ummar Najeriya dasu goya masa baya domin kawo karshen cin hanci a kasar nan," inji shi.

DUBA WANNAN: Bambanci tsakanin Siyasar Santsi da Tabo

Shugaban ya bayyana cewar hukumar 'yan sanda zata cigaba da goyawa hukumar yaki da cin hanci rashawa ta kowacce hanya, domin samun damar kwato duk kudaden da aka sace a kasar nan, domin ayi amfani da kudaden wurin cigaban kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel