Tsohuwar kakakin hukumar DSS, Marilyn Ogar ta maka gwamnatin tarayya a kotu

Tsohuwar kakakin hukumar DSS, Marilyn Ogar ta maka gwamnatin tarayya a kotu

- Tsohuwar mai magana da yawun hukumar yan sandan DSS, Marilyn Ogar, ta ki amincewa da murabus din da hukumar tayi mata

- Ogar tana bukatar kotu ta umurci hukumar ta mayar da ita bakin aikinta kuma ta sanya hukumar ta janye rage mata mukami da kayi daga deputy director zuwa assistant director

Tsohuwar kakakin hukumar yan sandan farin hula na DSS, Marilyn Ogar ta shigar da kara wani kotun ma'aikata inda ta ke Abuja inda ta ke jayaya da murabus din tilas da hukumar tayi mata a Satumban shekarar 2015.

An yi wa Oga murabus ne tare da wasu ma'aikata guda 14 a shekarar 2015, shekaru bakwai kafin ainin lokacin yi mata murabus din.

Tsohuwar kakakin hukumar DSS, Marilyn Ogar ta maka hukumar a kotu

Tsohuwar kakakin hukumar DSS, Marilyn Ogar ta maka hukumar a kotu

KU KARANTA: An kama wasu 'yan sanda suna karban na goro a titi

Sai dai lokacin da kotu ta karanta karar a ranar Juma'a 11 ga watan May domin a ji ta bakin su, lauyoyin masu kare hukumar basu hallarci kotun ba.

Lauyan mai shigar da kara, Adeola Adedipe, ya sanar da kotu cewa an sanar da lauyoyin masu kare hukumar ta hanyar aike musu da sammaci.

Alkalin kotun, Justice Olufunke Anuwe, ta bayar da umurnin a sake aike wa lauyoyin wanda ake tuhuma da sammaci kuma ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yuni.

Ogar tana bukatar kotun ta umurci hukumar na DSS ta mayar da ita bakin aikinta, kazalika, hukumar ta janye rage mukamin da akayi mata daga deputy director zuwa assistan director.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel