Buhari yayi ta’aziyya ga kungiyar CAN kan mutuwar sakataren ta

Buhari yayi ta’aziyya ga kungiyar CAN kan mutuwar sakataren ta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya wajen yin alhinin mutuwar babban sakataren kungiyar kiristocin najeriy na kasa, Rev (Dr) Musa Asake.

Ta’aziyyar shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina ya saki a ranar Juma’a, 11 ga watan Mayu.

Da yake aika sakon gaisuwa ga iyalan mamacin shugaban kasar yayi addu’an Allah ya ba duk masu alhinin mutuwar mamacin juriya ya kuma ji kan marigayin.

Buhari yayi ta’aziyya ga kungiyar CAN kan mutuwar sakataren ta

Buhari yayi ta’aziyya ga kungiyar CAN kan mutuwar sakataren ta

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Babban sakataren kungiyar mabiya addinin kirista na Najeriya (CAN), Musa Asake ya rasu yau a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwan rashin lafiya.

Dan uwansa, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Jonathan Asake ne ya sanar da jaridar Punch cewa Musa ya rasu a safiyar yau Juma'a 11 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda aka binne Marigayi Isyaka Rabiu a Kano (hotuna)

Musa Atake ya rasu ne bayan ya jagoranci zanga-zangar lumana na kungiyar CAN game da yadda wasu ta ake tsamanin makiyaya ne ke kashe kiristoci a wasu sassan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel