Da duminsa: Sakatare Janar na kungiyar CAN, Musa Asake, ya rasu

Da duminsa: Sakatare Janar na kungiyar CAN, Musa Asake, ya rasu

Babban sakataren kungiyar mabiya addinin kirista na Najeriya (CAN), Musa Asake ya rasu yau a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwan rashin lafiya.

Dan uwansa, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Jonathan Asake ne ya sanar da jaridar Punch cewa Musa ya rasu a safiyar yau Juma'a 11 ga watan Mayu.

Da duminsa: Sakatare Janar na kungiyar CAN, Musa Asake, ya rasu

Da duminsa: Sakatare Janar na kungiyar CAN, Musa Asake, ya rasu

"Ya rasu a safiyar yau. A halin yanzu muna dakin ajiye gawa na asibiti. In tare dashi a gidansa a jiya Alhamis," Inji shi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

Musa Atake ya rasu ne bayan ya jagoranci zanga-zangar lumana na kungiyar CAN game da yadda wasu ta ake tsamanin makiyaya ne ke kashe kiristoci a wasu sassan Najeriya.

Marigayin dai an asalin yankin kudancin Kaduna ne kuma yana daya daga cikin wadanda suke fafutukar ganin cewa ba'a take hakkin kirista ba a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel