An kama wasu 'yan sanda suna karban na goro a titi

An kama wasu 'yan sanda suna karban na goro a titi

An yiwa wasu jami'an yan sanda masu aikin kiyaye haddura a titi diran mikiya yayin da suke karaban na goro a hannun masu motoccin hawa a babban titin Thika-Garissa da ke kasar Kenya.

Jami'ai daga hukumar da'a da yaki da rashawa na kasar Kenya (EACC) ne suka taso keyar yan sandan yayin da suka kafa shinge a kan titin Ngoliba a yammacin ranar Alhamis suna cin karensu ba babaka.

An kama wasu 'yan sanda suna karban na goro a titi

An kama wasu 'yan sanda suna karban na goro a titi

Kamar yadda Standard Kenya ta ruwaito, Mataimakin manajan hukumar yaki da rashawar kasar (EACC), Urther Opilis ya ce an kama yan sandan uku ne sakamakon korafe-korafe da masu abin hawa da suka saba bin hanyar suka rika kaiwa hukumar.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

Wadanda aka kama sun hada da Muriuki Kimathi, George Gathirwa da Daniel Ndirangu dukkansu jami'ai ne masu mukamin Constables da ke aiki da Caji ofis na Ngiliba da ke gabashin Thika a lardin Kiambu.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishin EACC, Opilis ya ce Ndirangu ya tsere yayin da ake zo kama su amma daga bisani an kamo shi misalin karfe 4 na yamma.

"Bayan an duba aljihunsu, an sami jimlan kudi Sh18,800 daga hannun Kimathi da Gathirwa yayin da shi Ndirangu ya ranta a na kare," inji Opili.

Ya ce za'a gurfanar da su a gaban kuliya da zarar an kammala bincike a kansu.

Makonni 3 da suka gabata, an kama wasu jami'an yan sandan da ke aiki a caji ofis na Machakos na karbar na goro a hannun masu ababen hawa a Kathome kan titin Machakos-Nairobi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel