Nasarori 3 da shugaba Buhari ya samu a mulkin sa - Lai Mohammed

Nasarori 3 da shugaba Buhari ya samu a mulkin sa - Lai Mohammed

Babban ministan yada labarai da al'adu na tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya bayyanawa al'ummar duniya baki daya cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da cikakkiyar lafiyar da zai cigaba da jagorantar Najeriya har shekarar 2023.

Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan ikirarin ne a yayin wata ziyarar aiki da yake kaiwa a manyan kafafen yada labarai na duniya a kasar Amurka inda ya kuma ayyana cewa shugaban ya samu nasara sosai a mulkin sa.

Nasarori 3 da shugaba Buhari ya samu a mulkin sa - Lai Mohammed

Nasarori 3 da shugaba Buhari ya samu a mulkin sa - Lai Mohammed

Legit.ng ta samu cewa Lai Mohammed ya bayyana bangarori uku da suka hada da:

1. Harkar tsaro,

2. Yakar cin hanci da rashawa da kuma

3. Samar wa da al'umma aikin yi musamman matasa a matsayin nasarorin da shugaban ya samu.

A wani labarin kuma, Hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da harkokin ma'adanan ruwa da binciken su watau Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA a takaice a ranar Alhamis din da ta gabata ta zayyana cewa kananan hukumomi 380 ne a cikin jahohi 35 za su fuskancin ambaliyar ruwa a daminar bana.

Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta Nigeria Hydrological Services Agency ta kuma bayyana cewa akalla kananan hukumomi 78 ne za su fuskanci matsalar ambaliyar sosai fiye da sauran.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel