Jahohi 35 za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan daminar - Gwamnatin tarayya

Jahohi 35 za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan daminar - Gwamnatin tarayya

Hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da harkokin ma'adanan ruwa da binciken su watau Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA a takaice a ranar Alhamis din da ta gabata ta zayyana cewa kananan hukumomi 380 ne a cikin jahohi 35 za su fuskancin ambaliyar ruwa a daminar bana.

Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta Nigeria Hydrological Services Agency ta kuma bayyana cewa akalla kananan hukumomi 78 ne za su fuskanci matsalar ambaliyar sosai fiye da sauran.

Jahohi 35 za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan daminar - Gwamnatin tarayya

Jahohi 35 za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan daminar - Gwamnatin tarayya

Legit.ng ta samu cewa tuni dai hukumar ta NIHSA suka ankarar da gwamnatocin da lamarin ya shafi da nufin tunkarar bala'in tare kuma da rage radadin da hakan zai haifar.

A wani labarin kuma, Wata gawurtacciyar Hajiya mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Hajiya Abu Musa wadda aka fi sani da Mata Masu shaye-shaye yanzu haka tayi batan dabo a jihar Kebbi bayan ta sulalewa jami'an hukuma.

Shugaban hukumar nan dai ta gwamnatin tarayya dake hana sha da shafarar miyagun kwayoyi watau National Drgs Law Enforcement Agency (NDLEA) turance na jihar Kebbi dake yankin Arewa ta yamma mai suna Alhaji Suleiman Jadi shine ya sanar da hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel