Ministocin Buhari 5 da ke son tsayawa zama gwamnonin jihar su

Ministocin Buhari 5 da ke son tsayawa zama gwamnonin jihar su

Hakika dai tuni masu lura da al'amurran yau da kullum suka yi amannar cewa an kada gangar siyasar zabukan game gari na 2019 mai zuwa musamman ma dai duba da yadda harkokin siyasar suke ta kara daukar zafi.

Haka zalika kamar dai yadda aka saba a bisa al'ada dukkan gwamnan dake ci to yakan sake neman karin wa'adin shekaru hudu na mulkin sa wanda daga nan ne kuma kundin tsarin mulki ya zartar da cewa ba zai sake iya nema ba.

Ministocin Buhari 5 da ke son tsayawa zama gwamnonin jihar su

Ministocin Buhari 5 da ke son tsayawa zama gwamnonin jihar su

KU KARANTA: Jam'iyyu 17 za su yi wa Buhari taron dangi a 2019

A hannu guda kuma, akan samu zazzafar siyasa musamman a jihohin da gwamnonin su ke a wa'adin karshe na mulkin su wanda kuma lamarin kan kara zafi idan akwai wani babban minista daga jihar.

Legit.ng dai kamar kullum ta tattaro maku wasu daga cikin inda ake sa ran ministocin shugaba Buhari za su nemi kujerar gwamnan jihar su

1. Solomon Dalung - Ministan wasanni ne kma yana neman kujerar gwamnan jihar Filato

2. Kayode Fayemi - Ministan Ma'adanai kuma yana neman kujerar gwamnan jihar Ekiti

3. Aisha Alhassan - Ministar mat ce kuma tana neman kujerar gwamnan jihr Taraba

4. Adebayo Shittu - Ministan sadarwa kuma yana nman gwamnan jihar Oyo

5. Mansur Dan Ali - Ministan tsaro kuma yana neman kujerar gwamnan jihar Zamfara

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel