Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugabannin jam'iyyar APC na jihar Imo suka yi ganawar sirrance tare da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa ta Villa dake birnin tarayya ba tare da gwamnan jihar ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, an yi wannan ganawa ne ba tare da gwamna Rochas Okorocha na jihar wadda ta hadar da; shugaban jam'iyya na jihar, sakataren jam'iyya, mataimakin gwamnan, Sanata Benjamin Uwajumogu da Sanata Ifeanyi Ararume tare da wasu kwamishinoni.

Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin wannan ganawa ta sirrance gwamna Okorocha yana fadar mataimakin shugaban kasar sai ko kadan ba a dama ta dashi ba wanda daman tuni suke takun saka da shugabannin jam'iyyar tun wani taron jam'iyya da aka shirya gudanarwa a ranar 2 ga watan Mayu.

KARANTA KUMA: Kungiyar SOKAPU ta yi kira akan gurfanar da El-Rufa'i bisa laifin Kalaman nuna Kiyayya

Kamar yadda shafin jaridar The Guardian ya ruwaito, ba a gudanar da taron jam'iyyar kamar yadda aka shirya gudanarwa sakamakon rashin ga maciji dake tsakanin gwamnan da shugabannin jam'iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamna Okorocha ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a mahaifar sa ta garin Daura, inda yanzu kuma yake neman goyon bayan mataimakin shugaban kasa akan hana gudanar da wannan taro na jam'iyya a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel