Jam'iyyar APC ta raina wa 'yan Najeriya wayyo - Obasanjo

Jam'iyyar APC ta raina wa 'yan Najeriya wayyo - Obasanjo

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Aremu Obasanjo ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta mayar da 'yan Najeriya sakarkaru duba ga yadda ba abinda ta ke tabukawa don inganta rayuwarsu.

Obasanjo ya furta wannan magana ne a ranar Alhamis yayin da ya ke zanatawa da manema labarai a dakin karatu da ke gidansa a Abeokuta.

A yayin da ya ke cigaba da cacakar jam'iyyar mai mulki, tsohon shugaban kasan ya ce a halin yanzu mutanen Najeriya sun kara dilmiya wa cikin talauci fiye da yadda suke kafin zuwan wannan gwamnatin.

Jam'iyyar APC ta raina wa 'yan Najeriya wayyo - Obasanjo

Jam'iyyar APC ta raina wa 'yan Najeriya wayyo - Obasanjo
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

Ya kuma yi korafi kan yadda gwamnatin APC ta ke kara ciyo bashi daga kasashen waje inda ya ce bashin kasar ya karu daga biliyan $3.6 inda a yanzu ya haura biliyan $18 wanda jikokin mu ne za su biya basusukan a gaba.

Obasanjo kuma ya yi ikirarin cewa gwamnatin APC ta raba kan mutane ta hanyar amfani da addini da kabilanci wanda hakan abin takaici ne matuka. Ya kara da cewa, "Babu wanda ya ke da kwanciyar hankali a kasar."

Obasanjo kuma ya yi kuma bayyana sabuwar jam'iyyar da zai kafa na African Democratic Congress wanda ya ce za tayi maraba da dukkan mutanen Najeriya masu sha'awar ganin an kawo canji da cigaba mai ma'ana a kasar.

Obasanjo ya gargadi al'umma da su guji shiga jam'iyoyin APC da PDP duk da kwaskwarimar da suke kokarin yiwa jam'iyoyin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel