Jihar Akwa-Ibom ta fi kowace Jiha samun kudin shiga daga Gwamnatin Tarayya

Jihar Akwa-Ibom ta fi kowace Jiha samun kudin shiga daga Gwamnatin Tarayya

Hukumar NEITI da ke bin diddikin abin da Najeriya ta samu a fannin man fetur ta bayyana cewa a cikin watanni 3 Najeriya ta kashe abin da ya kusa kai Naira Tiriliyan 2 a wannan shekarar a wani rahoto.

A farkon watanni 3 na wannan shekarar, Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomin Najeriya sun raba Naira Tiriliyan 1.938 ini Hykumar NEITI. Hakan dai na nufin abin da Najeriya ta samu ya karu idan aka kamanta da bara.

Jihar Akwa-Ibom ta fi kowace Jiha samun kudin shiga daga Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta raba kusan Tiriliyan 2 a watanni 3

A shekarar 2017 abin da Najeriya ta samu a irin wannan lokaci shi ne Tiriliyan 1.411. A farkon watannin 2016 kuwa abin da Najeriya ta samu duk bai wyce Tiriliyan 1.132. An samu karin sama da kashi 70% na abin da aka samu a 2016.

Daga cikin kudin da aka samu a farkon bana, an rabawa Jihohin Kasar Naira Biliyan 655 sannan kuma aka ba kananan hukumomi 774 na kasar kusan Naira Biliyan 400. Gwamnatin Tarayya kuwa ta dauki sama da Naira Biliyan 800 daga kason.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun yi wani taro a Maiduguri

Idan aka bi filla-filla kuwa za a ga cewa a Watan Junairu, Najeriya ta raba Biliyan 655. A watan Fubrairu kuwa an samu Biliyan 647. A Watan uku watau Maris an raba Biliyan 647. Dr. Orji Ogbonnoya Orji na Hukumar ne ya fitar da wannan.

Rahoton ya nuna cewa Jihar Akwa-Ibom ce ta fi kowane samun kudin shiga daga abin da aka samu. Akwa-Ibom ta tashi da Naira Biliyan 50 daga Gwamnatin Tarayya yayin da Jihar Osun ta samu abin da bai kai Naira Biliyan 5 ba a wannan lokacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel