Osinbajo ya gaza dinke barakar da ta barke a Jam’iyyar APC a Imo

Osinbajo ya gaza dinke barakar da ta barke a Jam’iyyar APC a Imo

Zaben shugabannin Jam’iyyar APC da aka yi kwanaki ya bar baya da kura a irin su Jihar Imo da Kaduna da Ekiti da sauran su. Bayan nan kuma maganar wanda zai gaji Gwamna Rochas Okorocha a Jihar Imo tayi kamari.

Osinbajo ya gaza dinke barakar da ta barke a Jam’iyyar APC a Imo

Rochas Okorocha na kokarin daura surukin sa ya zama Gwamna

Yanzu haka ana ta kokarin sulhu tsakanin bangarorin Jam’iyyar APC tsakanin wadanda Gwamna mai-shirin barin gado yake goyon baya da sauran bangare amma abin ya ki yiwuwa. Gwamnan yana neman kakaba surukin sa ne a kujerar.

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da kan sa yayi kokarin sasanta bangarorin APC a Jihar Imo a jiya da dare amma abin ya faskara har aka gaji aka tashi kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust ta kasar nan.

KU KARANTA: Ojudu ya fasa takarar Gwamnan Jihar Ekiti a 2018

Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Mutanen Gwamna Rochas Okorocha watau Tawagar da ke bayan surukin Gwamna watau Uche Nwozu. Dayan bangaren shi ne na Mataimakin Gwamnan Jihar Eze Madumere da kuma Jama’ar sa a gefe.

Gwamnan dai ya yayi magana a fadar Shugaban kasa kwanakin baya inda yace za a kara zabe a Jihar Imo domin kuwa ba ayi zaben ba. Ifeanyi Ararume, Osita Izunaso, Benjamin Umajumogu da Theodore Ekechi ba su tare da Gwamna Okorocha.

Su dai bangaren Mataimakin Gwamnan Jihar Eze Madumere sun ce Jam’iyyar APC tayi zabe a makon jiya kuma sun nunawa Mataimakin Shugaban kasa hotuna da bidiyon wannan zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel