Gawar marigayi Sheikh Isiyaka Rabi'u ta iso Kano (hotuna)
Rahotanni sun kawo cewa gawar marigayi Sheikh Isiyaka Rabi’u ya iso gida Najeriya daga birnin Landan.
Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci dauko gawar a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano a safiyar yau Juma’a, 11 ga watan Mayu.
A yau ne dai za’ayi jana’izar Shehu malamin kuma babban attajirin Kano wanda ya rasu a birnin Landan bayan yayi fama da rashin lafiya.
KU KARANTA KUMA: 2019: Obasanjo ya zabi Jam’iyyar da zai shiga
Ga hotunan isowar gawar tasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng