Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da jami’an Yansanda guda 2, sun nemi miliyan 30

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da jami’an Yansanda guda 2, sun nemi miliyan 30

Wasu masu garkuwa da mutane da suka yi awon gaba da wasu jami’an Yansanda guda biyu a garin Fatakwal na jihar Ribas sun bukaci yanke ma rundunar Yansandan Najeriya nara miliyan Talatin a matsayin kudin fansar da suke bukata.

Jaridar Punch ta ruwaito Yansandan da aka sata sun hada da Sajan Haladu Muhammad da wani abokin aikinsa da ba’a bayyana sunansa ba, an sace su ne a ranar Laraba, 9 ga watan Mayu a masaukin da suka sauka, yayin da suka je yin wani aiki na musamman a garin Fatakwal.

KU KARANTA: Kowa da kiwon da ta karbe shi: Yaron Ministan Buhari ya tsunduma harkar waka

Majiyar ta kara da cewa Yan bindigar sun tuntubi wani dan uwan Muhammed ne ta wayar tarho inda suka bukaci a biyasu makudan kudaden, sa’annan suka bashi damar yin waya da dan uwan nasa don ya tabbatar musu da cewa yana raye.

Turnuku: An yi kare jinni biri jinni a tsakanin Yansanda da al’ummar jihar Legas

Sufetan Yansanda

Sai dai zuwa yanzu rundunar Yansandan ba ta yi wani bayani ba game da lamarin. Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito mahaifin Sajan Muhammad, Alhaji Umar Arikiya ya tabbatar da satar yaron nasa, inda yace bai yi mamakin faruwar lamarin ba duba da irin aikinsa.

Amma Alhaji Arikiya, wanda shi ma tsohon dansanda ne ya bukaci rundunar Yansandan ta kara kaimi wajen nemo masa yaronsa tare da abokin aikin nasa. Sai dai mataimakin Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Aremu Adeniran ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da hakan.

A wani labarin kuma, Kungiyar kabilar Eggon ta bukaci yayanra dasu taimaka da addu’o’I don ganin Allah ya fito da Sajan Muhammad da abokin aikinsa, sa’annan sun bukaci Yansanda su dage wajen ganin sun ceto rayuwar Muhamamd da abokin nasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel