Yansanda sun bindige mutane 2 a wani karanbatta da suka yi da jama’a a Legas

Yansanda sun bindige mutane 2 a wani karanbatta da suka yi da jama’a a Legas

Hankali ya tashi a unuwar Ori Oke dake yankin Makoko na jihar legas sakamakon wata karanbatta da aka sha a tsakanin wasu yan bindiga, jami’an hukumar kwamitin kota kwana dake yaki da masu cinye filaye da kuma matasan unguwar, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutane biyu, Kola Iwalokun da Emola Julius sun rasa rayukansu a sanadiyyar wannan rikita rikita, sakamakon harbinsu da Yansandan suka yi, yayin da jama’a da dama suka samu rauni.

KU KARANTA: Kowa da kiwon da ta karbe shi: Yaron Ministan Buhari ya tsunduma harkar waka

Wannan fada ya taso ne a lokacin da jami’an hukumar suka banka wuta a wani coci dake dauke da gidaje da shaguna 15, sakamakon an ginasu a kan haramtaccen fili, kamar yadda jami’an hukumar suka yi ikirari.

Yansanda sun bindige mutane 2 a wani karanbatta da suka yi da jama’a a Legas

Rikicin

Majiyar ta ruwaito hakan ne ya harzuka matasan unguwar, inda suka shirya zanga zangar da ta kais u har zuwa ofishin Yansanda dake Unguwar Adekunle, inda suka lalata motoci da kayayyaki masu daraja, inda ganin haka ya sa Yansanda suka bude musu wuta, nan take biyu suka fadi matattu.

Wani mazaunin unguwar, Ayodele Akintimeyin yace Yansanda tare da jami’an hukumar sun shammaci jama’a ne, sakamakon rikici kan mallakar filin na gaban Kotu ana shari’a akansa, don haka basu taba tsammanin za’a fatattaki mazauna gidan ba.

“Mutane na zama a gidajensu sama da shekaru 70, kwatsam da rana tsaka sai wasu mutane suka fara ikirarin wai filinsu ne, duk da an kai kara basu yarda, shi ne suka dauko Yansanda cikin motoci guda 20, inda suka kona coci, dakuna da shagunan da aka gina a filin.” Inji shi.

Sai dai wani jami’i a shelkwatar Yansandan farin kaya, ya bayyana cewa sun tafi aikin hadin gwiwa ne da jami’an hukumar yaki da cinye filaye a unguwar Makoko, inda matasan unguwar suka fara kai musu hari, suka raka su har ofishin Yansanda dake unguwar, sa’annan suka kona motocin Yansandan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel