Makashin maza, maka ke kashe shi: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a jihar Zamfara

Makashin maza, maka ke kashe shi: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a jihar Zamfara

Kimanin yan bindiga guda takwas ne suka gamu da ajalinsu a hannun jami’an rundunar Sojin Najeriya dake girke a garin Gusau, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan arangama ya faru ne a karamar hukumar Maru, inda Sojoji suke aiki na musamman don kakkabe yan bindiga da suka addabi al’ummar jihar da kashe kashe da sace sace.

KU KARANTA: Yan bindiga sun hallaka mutane 3 yayin da suka kai wani mummunan hari a Masallaci

Mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar Sojin kasa, Manjo Clement Abiade ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 10 ga watan Mayu a garin Gusau, inda yace mayakan Sojin kasa na gudanar da aikin ‘Operation idon raini.”

A cewarsa, Sojojin sun ci karo da yan bindigan ne a dazukan garin Dansadau, Kabaro da Sangeko, dukkaninsu a cikin karamar hukumar Maru, ya kara da cewa: “Bayan da wadanda muka kashe, sauran sun tsere da rauni a jikinsu.

“Mun san zuwa yanzu zasu fara neman agajin a sakamakon ciwuwukan da suka samu, don haka muke kira ga jama’a dasu taimaka mana da bayanan sirri da zasu bamu nasarar cafke yan bindigan nan, tare da sauran miyagu dake kashe mutanu babu gaira babu dalili.” Inji shi.

Daga karshe Manjo Clement ya bayyana cewa sun kwato babura guda biyar tare da alburusai da dama da gungun yan bindigar suka yara a lokacin da suke tsere.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel