Jami’an Sojoji sun yi galaba kan ‘Yan ta’adda a cikin Jihar Adamawa

Jami’an Sojoji sun yi galaba kan ‘Yan ta’adda a cikin Jihar Adamawa

- Rundunar Sojin kasar da ke Numan sun takawa wasu tsageru burki

- Yanzu haka Makiyayan sun addabi jama’a Yankin Arewacin kasar

- An damke wani Makiyayin an kuma yi nasarar karbe makaman su

Labari ya zo mana daga Rundunar Sojojin Najeriya cewa wasu Makiyaya da ke tada zaune-tsaye a Arewacin Najeriya sun ga ta kan su bayan da Sojin kasar su ka duran masu a Garin Numan.

Jami’an Sojoji sun yi galaba kan ‘Yan ta’adda a cikin Jihar Adamawa

Sojoji sun yi maganin wasu Makiyaya da ke ta’addanci a Najeriya

Darektan yada labarai na Sojojin Najeriya watau Birgediya Janar Texas Chukwu yace Sojojin kasar sun yi ram da Makiyaya kusan 10 da ke tada fitina a bangaren Adamawa inda su ka shiga buda masu wuta na sama da awa guda.

KU KARANTA: Wani Basarake ya nemi a rusa gidajen gumaka a Kasar sa

A ba-ta-kashin da aka yi an karbe makamai iri-iri wanda su ka hada da katuwar bindiga mai lugude da kuma kananan bindigogi da harsashi kirar NATO da kuma adda. Bayan nan kuma wani daga cikin su mai suna Adamu Umar ya shiga hannu.

Daga cikin abubuwan da aka samu har da wasu Babura 18 na zirga-zirga. Janar Texas Chukwu yace Sojojin na Najeriya na cigaba da neman hadin kan jama’a domin kawo zaman lafiya a kasar

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel