Tsohon Gwamnan Filato ya shiga hannun Hukumar EFCC

Tsohon Gwamnan Filato ya shiga hannun Hukumar EFCC

- Hukumar EFCC na zargin Sanatan PDP Jonah Jang da laifin sata

- Sanata Jonah D. Jang shi ma ya maka Hukumar EFCC kara a kotu

- Ana zargin Sanatan na PDP da yin gaba da sama da Naira Biliyan 6

Hukumar EFCC ta damke tsohon Gwamnan Filato watau Jonah Jang bisa zargin ya ci wasu kudi lokacin yana kujerar Gwamna. Sai dai tsohon Gwamnan ya maka Hukumar kara na tsare shi da tayi na dogon lokaci babu dalili.

Tsohon Gwamnan Filato ya shiga hannun Hukumar EFCC

Hukumar EFCC na zargin Sanata Jonah Jang da sata

EFCC ta maka Sanatan Jihar Filato Jonah Jang a babban Kotun Tarayya da ke Abuja da kuma wani babban Kotun Kasar da ke Jos inda ake neman kama shi da laifi har 12. Ana zargin Gwamnan ya saci kudin da su ka haura Naira Biliyan 6.

KU KARANTA: Ibrahim Magu zai sa kafar wando daya da wani tsohon Gwamna

Sai dai shi ma Gwamnan ya kai Hukumar da ke yaki da masu satar dukiyar kasa watau EFCC kara a Kotu. Jang yace babu dalilin da zai sa EFCC ta tsare sa fiye da sa’a 24 ba tare da ta kai shi gaban alkali ba don haka ya bukaci a biya sa wasu kudi.

Tuni dai Hukumar EFCC ta shigar da Sanatan na PDP a Kotu inda tace zai yi bayani. Hukumar tace ta gayyaci Jonah Jang ya amsa wasu tambayoyi ne amma ya gaza. Ko a kwanaki dai Hukumar ICPC ta kasar ta taso tsohon Gwamnan a gaba.

Dazu kun ji cewa Hukumar tana zargin tsohon Gwamnan Jihar Oyo watau Sanata Rashidi Ladoja da yin awon-gaba da wasu kudi kusan Biliyan 2 a 2007 lokacin yana kujerar Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel