Wani tsohon Gwamna Oyo da ‘Yan uwan sa sun cinye Biliyan 1.9

Wani tsohon Gwamna Oyo da ‘Yan uwan sa sun cinye Biliyan 1.9

- Hukumar EFCC ta izo keyar tsohon Gwamnan Jihar Oyo Ladoja

- Ana zargin Sen. Rashidi Ladoja da saida wasu hannun jarin Jihar

- An saida hannun jarin ba bisa ka’ida ba kuma an yi gaba da kudin

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa tana zargin tsohon Gwamnan Jihar Oyo watau Sanata Rashidi Ladoja da yin awon-gaba da wasu kudi har kusan Naira Biliyan 2 a 2007 lokacin yana kujerar Gwamna.

Wani tsohon Gwamna Oyo da ‘Yan uwan sa sun cinye Biliyan 1.9

Ana zargin Rashidi Ladoja da karkatar da kudin Oyo

EFCC tana zargin cewa tsohon Gwamnan na Oyo Rashidi Ladoja ya tattara yayi gaba da abin da aka samu lokacin da aka saida wasu hannun-jarin Jihar Oyo a sa'ilin yana Gwamna. EFCC tace Ladoja da ‘Yanuwan sa sun cinye wannan kudin.

Abubakar Madaki wanda wani babban Jami’in EFCC ne da ya binciki tsohon Gwamnan ya bayyanawa Kotu cewa Sanata Ladoja ya saida wasu hannun-jarin Jihar na kusan Biliyan 6.6 inda ya karkatar da wasu daga cikin wannan kudi.

KU KARANTA: Zaben 2019: Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya zabi wata Jam'iyya

Jami’in na EFCC ya fadawa Alkali mai shari’a a babban Kotun Tarayya ne Legas cewa Ladoja ya saida hannun jarin ne ba tare da iznin Majalisar sa ba. Akalla Naira Biliyan 1.9 dai ba su dawo asusun Gwamnatin Jihar ba inji Hukumar EFCC.

Kun ji jiya wata Kotu tace a maida Sanatan da aka dakatar daga Majalisa bakin aiki. Kotu ta fadawa Bukola Saraki ayi maza a dawo da Sanata Ovie Omo-Agege. ‘Dan Majalisar da ke bayan goyon bayan Shugaba Buhari a Majalisa yayi nasara a Kotu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel