Hadimin Shugaba Buhari, Odudu ya janye takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Ekiti

Hadimin Shugaba Buhari, Odudu ya janye takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Ekiti

A ranar Alhamis din da ta gabata Sanata Babafemi Ojudu, babban mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin siyasa ya janye takarar sa ta kujerar gwamnan jihar Ekiti.

Ojudu wanda ya kasance cikin masu neman jam'iyyar su ta APC ta fitar su a matsayin 'yan takara na jam'iyyar ya bayyana wannan hukunci a jiya Alhamis a babban birnin Ado-Ekiti.

Hadimin na shugaba Buhari ya zargi shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun da nuna rinjayen goyon bayan kan wani dan takara a yayin fitar da dan takara na jam'iyyar.

Legit.ng ta fahimci cewa, Ojudu ya janye kudirin sa na takara gabannin zaben gwamna da hukumar zabe ta kasa ta shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Yuli.

Hadimin Shugaba Buhari, Odudu ya janye takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Ekiti

Hadimin Shugaba Buhari, Odudu ya janye takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Ekiti

Cikin dalilai da Ojudu ya bayar na janye takarar sa ya bayyana cewa, ba zai lamunci zubar da jinin al'umma ba domin cimma manufa ta kasancewa gwamna ba, wanda ya nemi wannan kujera ne da manufar ceto al'ummar jihar Ekiti daga cikin kangi na talauci da mulkin kama karya da suka sha fama.

KARANTA KUMA: Oshiomhole ya bayyana kudirin neman Kujerar Shugaban jam'iyyar APC

Hakazalika kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, mashawarcin na shugaban kasa ya jaddada cewa ba zai gushe ba wajen yiwa al'ummar jihar hidima gami da godiya a gare su dangane da goyon baya da suka nuna a gare shi tun daga fari har zuwa yanzu.

A yayin da ya ke jinjina da yabawa wasu shugabannin jam'iyyar su ta APC dangane da rawar da suka taka wajen kwantar da duk wata tarzoma da ta kunno kai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Ojudu ya yi yabo na musamman ga jagorori na yankin Kudu maso Yamma da suka hadar da; Asiwaju Bola Tinubu, Cif Bisi Akande, Cif Segun Osoba da makamantan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel