Kungiyar SOKAPU ta yi kira akan gurfanar da El-Rufa'i bisa laifin Kalaman nuna Kiyayya

Kungiyar SOKAPU ta yi kira akan gurfanar da El-Rufa'i bisa laifin Kalaman nuna Kiyayya

Wata kungiya ta al'ummar Kudancin jihar Kaduna SOKAPU (Southern Kaduna Peopples’ Union) ta yi kira akan a dauki mataki akan gwamnan jihar Mallam Nasir EL-Rufa'i, bisa laifin sabawa dokar kasa ta cin mutunci ba tare da yiwa bakin sa linzami ba.

Kungiyar da sanadin shugaban ta, Barr. Solomon Musa ya kira akan ayi azamar cafkewa gami da gurfanar da gwamnan jihar na Kaduna bisa kalaman sa na nuna kiyayya wanda sabawa dokar kasan nan ne.

Gwamnan a kwana-kwanan nan ya cin mutunci da kausasa harshen sa akan Sanatocin masu wakiltar jihar a majalisar dattawa da suka hadar da; Suleiman Othman Hunkuyi, Shehu Sani da kuma Dajuma Laah.

Kungiyar SOKAPU ta yi kira akan gurfanar da El-Rufa'i bisa laifin Kalaman nuna Kiyayya

Kungiyar SOKAPU ta yi kira akan gurfanar da El-Rufa'i bisa laifin Kalaman nuna Kiyayya

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Daily Post ya bayyana gwamnan ya kuma kirayi al'ummar jihar sa ta Kaduna akan kai hari na caccaka ga Dattawan jihar.

KARANTA KUMA: Dokar hana Fataucin Maganin Tari: Hukumar NDLEA ta cafke miyagu 17 a jihar Kwara

A yayin ganawa a taron kwamitin kawo zaman lafiya tare da dukkanin masu ruwa da tsaki wanda cibiyar Global Peace Foundation ta Najeriya ta shirya, shugaban kungiyar ya bayyana cewa akwai bukatar a gurfanar da gwamnan cikin gaggawa domin ya zamto izina ga masu yiwa zaman lafiya zagon kasa a fadin jihar.

Barr. Solomon ya bayyana damuwar sa kwarai da aniyya dangane da yadda manyan 'yan siyasa musamman gwamna El-Rufa'i ke gaza yiwa bakin sa linzama wajen furta kalamai da ka iya janyo rikici a kasar wanda ya kamata hukumomi tsaro su dauki mataki a kansa da ire-iren sa.

Saura masu ruwa da tsakin da suka tofa albarkacin bakin su a taron sun yi tir gami da Allah-wadai ga kalaman gwamnan wanda ka iya janyo barazana ga tsaro da kuma zaman lafiya a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel