Oshiomhole ya bayyana kudirin neman Kujerar Shugaban jam'iyyar APC

Oshiomhole ya bayyana kudirin neman Kujerar Shugaban jam'iyyar APC

A ranar Alhamis din da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshionhole, ya bayyana kudirin sa a babban birnin tarayya na tsayawa takara ta kujerar shugaban jam'iyyar APC kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya bayyana.

A halin yanzu dai Oshiomhole shine dan takara daya tilo da ka iya gumurzu da shugaban jam'iyyar mai ci, Cif John Odigie-Oyegun muddin ya yanke shawara ta sake tsayawa takarar kujerar sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, dukkanin su biiyu haifaffun jihar Edo ne kuma kowanen su ya kasance tsohon gwamna a jihar.

Oshiomhole ya bayyana kudirin neman Kujerar Shugaban jam'iyyar APC

Oshiomhole ya bayyana kudirin neman Kujerar Shugaban jam'iyyar APC

Rahotanni sun bayyana cewa, an tashi uwar watsi yayin wata ganawa da shugabannin jam'iyyar na jihar da kuma na yankin Kudu maso Kudancin kasar nan sakamakon kudurin tsaffin gwamnonin biyu.

KARANTA KUMA: Wani Mai Laifi ya yiwa Alkaliyar Kotu Barazanar ta yi kankanta ta tura shi Gidan Wakafi

A halin yanzu dai Oshiomhole na da rinjayen dama sakamakon goyon bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi masa.

Haka zalika, ana kuma sa ran Oshiomhole zai samu goyon baya na kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, wanda wannan doriya ce akan rinjaye na samun dama wajen nasarar lashe kujera ta shugaban jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel