Shugaban kasa ya zargi makiyaya da yunkurin ganin bayan shi zaben 2019

Shugaban kasa ya zargi makiyaya da yunkurin ganin bayan shi zaben 2019

Fadar shugaban kasar Najeriya ta zargi makiyan kasar da yunkurin bata sunan Shugaba Muhammadu Buhari domin ganin ya fadi a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Wannan zargin dai ya fito ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasar Mista Femi Adesina inda ya kuma kara da cewa wasu mutane na sauya ma'anar kalaman shugaban da jirkita su domin cimma manufar su ta siyasa.

Shugaban kasa ya zargi makiyaya da yunkurin ganin bayan shi zaben 2019

Shugaban kasa ya zargi makiyaya da yunkurin ganin bayan shi zaben 2019

Legit.ng haka zalika ta samu cewa Mista Adesina ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani kan korafe-korafen da ake yi kan jinyar da shugaban ke zuwa Ingila.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ranar Talata da ta gabata ne dai Shugaban kasar Muhammadu Buhari, da yanzu haka yake da shekaru akalla 74 ya sake komawa kasar Ingila domin ganin likitocinsa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel