Zaben 2019: Jam'iyyu 17 sun yi hadin gwuiwar fitar da dan takara 1 da zai kada Buhari

Zaben 2019: Jam'iyyu 17 sun yi hadin gwuiwar fitar da dan takara 1 da zai kada Buhari

Akalla jam'iyyu 17 ne masu cikakkiya rijista da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa suka sanar da shirin su na yin hadin gwuiwa domin tunkarar zaben shekarar 2019.

Haka ma kuma gamayyar jam'iyyun sun ayyana shan alwashin su na fitar da dan takarar shugabancin kasa kwaya daya tilo da zai fuskanci shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin zaben.

Zaben 2019: Jam'iyyu 17 sun yi hadin gwuiwar fitar da dan takara 1 da zai kada Buhari

Zaben 2019: Jam'iyyu 17 sun yi hadin gwuiwar fitar da dan takara 1 da zai kada Buhari

KU KARANTA: Ban kara fitowa dan daudu a fim - Ado Gwanja

Legit.ng ta samu cewa gamayyar hadakar jam'iyyun haka zalika ta bayyana cewa har yanzu kofar ta a bude take ga dukkan masu son shiga hadakar majar tare da su.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta PDP kamar yadda muka samu kawo yanzu haka dai ta kammala shirin ta na yi kutungwilar tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ta da zai kara da shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Wannan dai kamar yadda muka samu, majiyar mu ta Vanguard ta ce ta samu tabbacin hakan ne daga wajen wani jigo a jam'iyyar wanda kuma ya bukaci a sakaya sunan sa a ranar Larabar da ta gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel