Za a rika ware kashi 1 cikin 100 na dukiyar Najeriya wajen harkar lafiya

Za a rika ware kashi 1 cikin 100 na dukiyar Najeriya wajen harkar lafiya

- Za a rika cire kashi 1% na dukiyar Najeriya domin habaka kiwon lafiya

- Shugaban Majalisar Dattawa yace sai inda karfin sa ya kare a kan hakan

- Yanzu haka dai ana fama da karancin Likitoci da kayan aiki a Najeriya

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya watau Sanata Bukola Saraki na kokarin ganin an inganta sha’anin kiwon lafiya a kasar ta hanyar ware makudan kudi domin kawo gyara.

Za a rika ware kashi 1 cikin 100 na dukiyar Najeriya wajen harkar lafiya

Shugaban Najeriya Buhari ya bar Kasar domin ya ga Likita

Akwai kudirin da ka yawo a Majalisar Najeriya na ganin cewa an dauki kashi 1% na dukiyar kasar an karkatar wajen gyara dakunan shan magani a kasar. Shugaban Majalisar Kasar yace zai yi bakin kokari na ganin an cin ma wannan.

KU KARANTA: Inyamuran Najeriya za su goyi bayan Shugaba Buhari

Bukola Saraki ya bayyana irin kokarin da su ke yi na ganin jama’a sun samu isasshen kula a asibiti. Shugaban Majalisar ya gana da Shugaban Hukumar da ke kula da gidajen shan magani watau NPHDA na kasar a ofishin sa a makon nan.

Tun a baya dai jama’a su ka nemi a rika kashe wani kaso na kudin da kasar ta mallaka domin inganta harkar lafiya. Yanzu haka dai ana fama da karancin Likitoci a kasar inda Likita 1 ke duba marasa lafiya akalla 6000 a fadin kasar.

Yanzu dai Shugaban Majalisar Dattawa Saraki ya bayyana inda karfin sa zai kare game da harkar kiwon lafiya a kasar. Dazu kun ji cewa Kotu ta fadawa Bukola Saraki ayi maza a dawo da Sanatan da aka dakatar kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel