Matan gwamnonin Arewa zasu kawo karshen wata matsala dake damun yankin

Matan gwamnonin Arewa zasu kawo karshen wata matsala dake damun yankin

Matan gwamnonin Arewacin Najeriya sun kafa wata cibiyar gyara da bayar da tallafi ga matasan da shan miyagun kwayoyi ya lalatawa rayuwa a Sokoto.

Matar gwamnan jihar Sokoto, Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal, c eta karbi bakuncin ragowar matan gwamnonin a taron su da suka saba yi duk bayan watanni hudu.

A wata sanarwa da suka fitar a karshen ganawar su a jiya, matan gwamnonin sun bayyana gamsuwar su da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakile yaduwa da kuma amfani da maganin tari mai dauke da sinadarin kodin da matasa ke amfani das hi ta mummunar hanya.

Matan gwamnonin Arewa zasu kawo karshen wata matsala dake damun yankin

Matan gwamnonin Arewa

A karshen ganawar ta su, matan gwamnonin sun kai ziyara gidan kayan gargajiya na marigayi Usman Danfodio da Waziri Umar.

DUBA WANNAN: Gwamnatin katsina ta rufe ofishin Glo a Jihar saboda kunnen kashi

Shugabar kungiyar matan kuma uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Abubakar, ta bayyana cewar cibiyar ta Sokoto ita ce ta biyu , bayan ta jihar Kebbi, da kungiyar ta samar domin tallafawa matasa da kuma reaba su da shaye-shaye.

Mai masaukin baki, Hajiya Mariya Tambuwal, ta jaddada bukatar hada karfi tsakanin gwamnatoci da masu ruwa da tsaki domin yaki da muguwar halayyar nan ta tu’ammali da kayan maye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel