Kishin-kishin: Jam'iyyar PDP ta kammala shirin zabar Atiku a matsayin dan takarar ta a 2019

Kishin-kishin: Jam'iyyar PDP ta kammala shirin zabar Atiku a matsayin dan takarar ta a 2019

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP kamar yadda muka samu kawo yanzu haka dai ta kammala shirin ta na yi kutungwilar tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ta da zai kara da shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Wannan dai kamar yadda muka samu, majiyar mu ta Vanguard ta ce ta samu tabbacin hakan ne daga wajen wani jigo a jam'iyyar wanda kuma ya bukaci a sakaya sunan sa a ranar Larabar da ta gabata.

Kishin-kishin: Jam'iyyar PDP ta kammala shirin zabar Atiku a matsayin dan takarar ta a 2019

Kishin-kishin: Jam'iyyar PDP ta kammala shirin zabar Atiku a matsayin dan takarar ta a 2019

KU KARANTA: Dan Najeria da ya kera injin din mota mafi gudu a duniya

Legit.ng ta samu cewa jigon jam'iyyar ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ta lura cewa Atiku Abubakar din ne kawai wanda yanzu ya fito da gaske kuma yake iya karawa da gwamnati.

A wani labarin kuma, Akalla jam'iyyu 17 ne masu cikakkiya rijista da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa suka sanar da shirin su na yin hadin gwuiwa domin tunkarar zaben shekarar 2019.

Haka ma kuma gamayyar jam'iyyun sun ayyana shan alwashin su na fitar da dan takarar shugabancin kasa kwaya daya tilo da zai fuskanci shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin zaben.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel