Shehu Sani ya soki zaben shugabannin APC da aka yi a Kaduna

Shehu Sani ya soki zaben shugabannin APC da aka yi a Kaduna

‘Dan Majalisar Dattawan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya watau Sanata Shehu Sani ya soki zaben shugabannin Jam’iyyar APC mai mulki da aka yi a makon jiya a Jihar Kaduna inda yace da sake.

Sanatan na Jam’iyyar APC yace ya kamata ace zaben da aka shirya ya kara nuna karfin tsarin damukaradiyya ne amma sai da ya nuna yadda wasu masu madafan iko a hannun su ke danne ‘Ya ‘yan Jam’iyya da karfin tsiya.

Shehu Sani ya soki zaben shugabannin APC da aka yi a Kaduna

Sanata Shehu Sani ya koka da tafiyar wasu a APC

Shehu Sani yayi amfani da shafin Tuwita inda ya koka da lamarin da yace wasu sun yi baba-kare da kaka-gida a zaben na APC. Sanatan ya nuna cewa akwai wasu da ke da fuskar mutanen kwarai amma da bakar zuciya a cikin APC.

KU KARANTA: An sa ranar shari'ar Sanata Dino Melaye a Kotu

‘Dan Majalisar ya soki zaben da aka yi a Jihar Kaduna inda ya nuna cewa ba zaben gaskiya aka yi ba. Kwanaki dai Sanatan Kaduna ta Arewa watau Suleiman Othman Hunkuyi ya bayyana cewa ba ayi zaben kwarai a Jihar ta Kaduna ba.

Sanata Shehu Sani yake cewa a Jam’iyyar ta APC akwai wasu da su na kiran canji ne kurum da baki amma a zuciyar su dai babu abin da ya canza. Gwamna Nasir El-Rufai wanda ba su jituwa da Sanatocin dai ya dawo APC ne bayan ya bar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel