Irin canjin da aka gani a Gwamnatin APC – Inji Hadimin Shugaban kasa

Irin canjin da aka gani a Gwamnatin APC – Inji Hadimin Shugaban kasa

A makon nan ne mu ka samu labari cewa daya daga cikin masu ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ya fadi kadan daga alherin Gwamnatin nan wanda yace daga ciki akwai samar da zaman lafiya da tsaro a Kasar.

Bashir Ahmaad wanda yake ba Shugaban Kasa Buhari shawara kan kafofin sadarwa na zamani yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda yace daga cikin alherin Gwamnatin Buhari yanzu ta kai ana iya yawo a jiragen kasa.

Irin canjin da aka gani a Gwamnatin APC – Inji Hadimin Shugaban kasa

Hadimin Buhari ya bayyana nasarorin Gwamnatin nan

Malam Ahmad yake cewa masu tafiya daga Birnin Tarayya Abuja zuwa Garin Kaduna za su iya amfani da jiragen kasan da Gwamnatin Buhari ta kawo. Idan ba ku manta ba Gwamnatin nan ta karasa aikin jirgin kasan da ta gada.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya koka da cewa wasu za su kashe APC

Bayan nan kuma Hadimin Shugaban kasar yace kwanan nan za a kamala aikin jirgin kasan Legas zuwa Garin Ibadan mai kilomita kusan 180. Yanzu haka dai an yi nisan gaske a aikin inda kowace rana ake cin akalla kilomita 1.2

Bashir yake cewa an samu zaman lafiya a Yankunan da Boko Haram su ka rika kai wa ta’adi a baya. Yanzu dai an samu karuwar zaman lafiya a Yankin Arewa-maso-gabashin kasar bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel