A karshe rundunar fatattakar Buhari sun lalubo jam’iyyara da zasu marawa baya

A karshe rundunar fatattakar Buhari sun lalubo jam’iyyara da zasu marawa baya

Rundunar fatattakar shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ke jagoranta ta samo jam'iyyar da zata goyawa baya don ganin hakan da suka sanya a gaba ya cimma gaci.

A karshe rundunar fatattakar Buhari sun lalubo jam’iyyara da zasu marawa baya

A karshe rundunar fatattakar Buhari sun lalubo jam’iyyara da zasu marawa baya

Wannan jam'iyya da suka amice su goyawa baya ita ce jam'iyyar African Democratic Congress.

Tsohon sugaban kasar ya sanar da hakan ne a jiya Laraba yayin taron manema labarai da ya gabatar a babban dakin karatu dake garin Abeokuta a jihar Ogun. Kamar yadda jaridar Independent ta rawaito.

KU KARANTA: Kotu ta ajiye hukuncin bayar da Dino Melaye beli zuwa ranar 16 ga watan Mayu

Kungiyar fafutukar dai babban abinda ta sanya a gaba shi ne fitar da shugaba Buhari daga fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cewar kungiyar shugaba Buhari ya gaza a saboda haka ba abu mai yiwuwa ba a cigaba da mara masa baya ba, a don haka suka kudiri aniyar lalubo wata jam'iyya da zasu marawa baya ddon ganin sun cimma burinsu.

Nan gaba kadan Legit.ng zata kawo muku cikakken rahoton yadda aka bi wajen fidda jam'iyyar da kuma sauran jawabai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel