Da duminsa: Kotu ta dawo da Sanata Omo-Agege bayan dakatar da shi na watanni 3

Da duminsa: Kotu ta dawo da Sanata Omo-Agege bayan dakatar da shi na watanni 3

- Bayan sato sa katsi tsakanin Majalisar Dattijai ta kasa, a karshe Sanata Omo-Agege yayi nasara

- Sai dai ya zuwa yanzu ba'a ji mai bangaren Majalisar zai ce dangane da wannan hukuncin ba

Wata babbar kotu dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta warware dakatarwar da aka yiwa Sanata mai wakiltar jihar Delta ta tsakiya Sanata Omo-Agege ta tsawon watanni uku.

Da duminsa: Kotu ta dawo da Sanata Omo-Agege bayan dakatar da shi na watanni 3

Da duminsa: Kotu ta dawo da Sanata Omo-Agege bayan dakatar da shi na watanni 3

Tun bayan dakatarwar da aka yi masa Sanatan ya nufi kotu domin kalubalantar matakin da Majalisar Dattijan ta dauka akansa, na dakatar da shi har tsawon kwanaki 90.

Karar ta shi dai ta hada da Majalisar da shugaban Majalisar Dr. Abubakar Bukola Saraki da kuma babban attony na kasar nan a cikin kundin karar ta sa mai lamba FHC/ABJ/CS/314/2018.

KU KARANTA: Dalilin dayasa muka shiga damuwa akan Buhari, APC – Sabuwar PDP

Da yake yanke hukunci yau Alhamis, mai shari’a Nnamdi Dimgba ya ce, dakatar da Sanatan ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar nan. Kotun ta ce ba dai-dai ba ne ga kwamitin ladabtarwa na Majalisar ya dakatar da Sanatan bayan ya riga da ya nemi afuwar Majlisar bisa kalaman da yayi akanta.

Da duminsa: Kotu ta dawo da Sanata Omo-Agege bayan dakatar da shi na watanni 3

Da duminsa: Kotu ta dawo da Sanata Omo-Agege bayan dakatar da shi na watanni 3

Mai shari’a Dimgba ya cigaba da cewa, dakatarwar da aka yiwa Sanatan ya saba da sashi na 4(8) da sashi na 6(6) na kundin tsarin mulkin 1999 na tarayyar Najeriya.

Kafin yanke hukuncin dai Kotun ta ki karbar rokon Majalisar da kuma shugaban Majalisar na cewa tayi watsi da karar domin bata da ikon sauraronta.

Bayan warware waccan dakatarwa da Majalisar tayi wa Sanatan, Kotun ta kuma umarci Majalisar da ta biya shi duk kannin albashinsa da kuma sauran alawus-alawus dinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel