An kama tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda da laifin damfara

An kama tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda da laifin damfara

- An gurfanar da tsohon Sufeto Janar din ' yan sanda, Sunday Ehindero, a gaban kotu a ranar Alhamis din nan. Tare da shi akwai tsohon kwamishinan 'yan sanda, John Obaniyi, an gurfanar dasu bisa kama su da laifuka shida na damfara

An kama tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda da laifin damfara

An kama tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda da laifin damfara

An gurfanar da tsohon Sufeto Janar din ' yan sanda, Sunday Ehindero, a gaban kotu a ranar Alhamis din nan. Tare da shi akwai tsohon kwamishinan 'yan sanda, John Obaniyi, an gurfanar dasu bisa kama su da laifuka shida na damfara.

An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Apo district High Court dake babban birnin tarayya, Abuja. Ana tuhumar su da laifin barnatar da Naira miliyan 578 wanda jihar Bayelsa ta bada don siyan makamai.

DUBA WANNAN: Tsoho dan shekara 92 ya zama shugaban kasa

Kamar yanda ake zargi, sun karkatar da kudin ne zuwa wani asusun banki wanda ya kasance mallakar wadanda ake zargi. Kudin sun samar da ribar Naira miliyan 16,412,315. Ribar kuma anyi amfani da ita ne ga bukatun wadanda ake tuhumar.

Ana kuma tuhumar su ne da laifin yi wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa karyar cewa ribar da aka samu anyi amfani da ita ne don hukumar.

Da kotu ta waiwayi wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake yi musu.

An gurfanar da Ehindero da Obaniyi a shekarar 2012 saboda zargin da ake yi musu. Sai kuma sun daukaka kara.

Bayan samun umarni daga kotun koli a watan Disamba, an kara kiran wadanda ake zargin don su fuskanci shari'a.

Bayan ban hakuri, kotun ta bada belinsu tare da dage sauraron karar zuwa 19 ga watan yuni.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel