Amurka ta ba Najeriya N32bn don gudanar da ƙididdigar masu cutar Kanjamau

Amurka ta ba Najeriya N32bn don gudanar da ƙididdigar masu cutar Kanjamau

Gwamnatin Kasar Amurka ta bayar da tallafin Naira Biliyan Talatin da Biyu domin gudanar da ƙididdiga da tantance adadin masu dauke da cutar ƙanjamau a fadin kasar Najeriya wanda za a fara aiwatar wa a watan Yuni mai gabatowa.

Ministan lafiya na kasa, Farfesa Isaac Adewole, shine ya bayyan hakan yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin ma'aikatar sa ta lafiya, cibiyar kare yaduwar cutar ƙanjamau ta ƙasa da kuma gwamnatin ƙasar Amurka a babban birnin tarayya.

A sanarwar ministan ta ranar yau Alhamis za a fara gudanar da ƙididdigar ne a watan gobe inda ake sa ran kammalawa cikin watannin shidda.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, za a gudanar da wannan kididdiga a gaba daya jihohi 36 na kasar nan gami da babban birnin tarayya na Abuja.

Ministan Lafiya; Farfesa Isaac Adewole

Ministan Lafiya; Farfesa Isaac Adewole

Wannan kididdiga mai lakanin 'Kididdigar Cutar Kanjamau da Tasirin ta a Najeriya' kamar yadda ministan ya bayyana za ta taimaka kwarai da aniyya wajen kawar da hasashen nauyenauyen dake tattare da cutar kanjamau a kasar nan.

KARANTA KUMA: Zambar N650m: Kotu ta kekashe akan bukatar Otiti ta ficewa daga Najeriya

Adewole ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta taimaka matuka yayin da ta malalo $90m tare da hadin gwiwar wasu cibiyoyi, inda ya ce kididdigar ba za ta takaita akan kanjamau kadai ba yayin da cututtuka masu alaka da koda na Hepatitis B da Hepatitis C za su dangana cikin ta.

Bayan kammaluwar wannan kididdiga za kuma a dora masu dauke da ita kan magani kamar yadda ministan ya bayyana yayin da ya kara da cewa za a wallafa sakamakon kididdiga domin kuwa siyasa ba za ta kusance ta ba.

A nasa jawabin jakadan Kasar Amurka zuwa Najeriya, Stuart Symington, ya kirayi 'yan Najeriya akan bayar da hadin kai yayin wannan kididdiga domin tabbatar da nasarar ta wajen gano matakai da za a daukarwa cutar kanjamau a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel