Kotu ta ajiye hukuncin bayar da Dino Melaye beli zuwa ranar 16 ga watan Mayu

Kotu ta ajiye hukuncin bayar da Dino Melaye beli zuwa ranar 16 ga watan Mayu

- Justice Nasiru Ajana, babban jojin jihar Kogi a daga bukatar Dino Melaye ta bayar dashi beli zuwa ranar Laraba 16 ga watan Mayu na shekarar 2018

- Dino Melaye, Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, ya kasance yana babban asibitin birnin tarayya tun satin da ya gabata

- Sanata Melaye wanda akace yana da ciwon asthma, yana samun kulawa a banagaren masu bukatar kulawar gaggawa a babban asibitin birnin tarayya

Justice Nasiru Ajana, babban jojin jihar Kogi a daga bukatar Dino Melaye ta bayar dashi beli zuwa ranar Laraba 16 ga watan Mayu na shekarar 2018.

Dino Melaye, Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, ya kasance yana babban asibitin birnin tarayya tun satin da ya gabata sakamakon fadowa da yayi daga motar ‘Yan Sanda.

Sanata Melaye wanda akace yana da ciwon asthma, yana samun kulawa a banagaren masu bukatar kulawar gaggawa (Intensive Care Unit, Trauma) a babban asibitin birnin tarayya.

KU KARANTA KUMA: PDP tayi Allah wadai da Sufeto Janar na yan sanda bisa akan kin amsa gayyatar majalisa

Sanatan ya samu matsala a jikinsa sakamakon barkonon tsohuwa da jami’an ‘Yan Sanda suka shaka masa lokacin da suka daukeshi zuwa Lokoja dake jihar Kogi a satin da ya gabata

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel