Ashe wasu 'yan Majalisa da jami'an Tsaro suka hada tuggu na sace Sandar Majalisa - Hukumar 'Yan sanda

Ashe wasu 'yan Majalisa da jami'an Tsaro suka hada tuggu na sace Sandar Majalisa - Hukumar 'Yan sanda

Da sanadin wallafar rahoto ta shafin jaridar The Punch da ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata, mun samu rahoton cewa ashe wasu 'yan majalisar da jami'an tsaro ke hannu cikin tuggu na sace sandar girma ta majalisar dokoki ta kasa.

Binciken dai ya tabbatar da cewa ashe wasu 'yan majalisa da jami'an tsaro suka kulla makirci gami tuggun sace sandar girma ta majalisar makonni uku da suka gabata.

Shugaban jami'an 'yan sanda na rukunin majalisar dokoki ta kasa dake birnin tarayya, CSP Sulu-Gambari Abdul, ya bayyana cewa harin da ya afku a farfajiyar majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Afrilun da ta gabata ba wani abu bane face tuggu da makirci irin na cikin gida.

Legit.ng ta fahimci cewa, Gambari ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamkon bincike akan lamarin da kwamitin hukumomin tsaro da na majalisar suka gudanar domin gano bakin zaren.

Ashe wasu 'yan Majalisa da jami'an Tsaro suka hada tuggu na sace Sandar Majalisa - Hukumar 'Yan sanda

Ashe wasu 'yan Majalisa da jami'an Tsaro suka hada tuggu na sace Sandar Majalisa - Hukumar 'Yan sanda

A cewar babban jami'in, sace sandar girma ta majalisar dokoki ta kasa tuggu ne da wadansu 'yan majalisar da jami'an tsaro suka kulla domin cimma manufa ta makirci, wanda bayan abinda bai wuci sa'o'i a shirin da hudu aka tsinto sandar karkashin wata gada a Abuja.

KARANTA KUMA: An Lakadawa Wani Barawon Nama duka har Lahira a kasar Zimbabwe

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin 'yan majalisar sun yi korafi tare da tofa albarkacin bakin su dangane da yadda za a kiyaye afkuwar hakan a gaba.

A yayin haka kuma wani babban dan sanda na rukunin majalisar dokoki, Mista Brighton Danwalex ya bayyana cewa, cikin binciken da aka gudanar ya yi nuni da yadda a yayin afkuwar harin Sanata Ali Ndume ya twatar da jami'an tsaro masu kare sandar girma akan kada su kuskura su kai hannu gare ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel