Bayan faɗuwa zaben fidda gwani, wani ɗan takadar gwamna ya fice daga PDP

Bayan faɗuwa zaben fidda gwani, wani ɗan takadar gwamna ya fice daga PDP

- Jam'iyyar PDP na cigaba da samun zaizayewar mambobinta gabannin zaben 2019

- Wani Jogo a Jam'iyyar ya sake ficewa amma bai bayyana wace jam'iyyar zai koma ba

Kwanaki biyu kacal da kayar da shi a zaɓen fidda gwani na Gwamnan jihar Ekiti a Jam'iyyar PDP Prince Dayo Adeyeye, ya bayyana ficewa daga PDP.

Bayan faɗuwa zaben fidda gwani, wani ɗan takadar gwamna ya fice daga PDP

Bayan faɗuwa zaben fidda gwani, wani ɗan takadar gwamna ya fice daga PDP

Zaɓen dai na fidda gwanin an gudanar da shi ne a ranar Talata inda Dayon yazo na biyu da ƙuri'u 771. A bisa wannan kayi da ya sha ne kuma Adeyeyen ya bayyanawa magoya bayansa hukuncin ficewa daga Jam'iyyar da yayi domin a cewarsa, Gwamnan jihar Ayodele Fayose ya shirya sanya jam'iyyar PDP cikin aljihun ne a jihar.

Sai dai kuma wani abu da har yanzu za'a so ji shi ne, jam'iyyar da zai koma domin har yanzu bai bayyana ina yake shirin komawa ba.

Sauya sheka dai ga ‘yan siyasa a Najeriya musamman a wannan lokaci ba abu ne sabo ko mai wahala ba, yau wani na iya shiga da safe da yamma kuma kaji an ce ya fice.

KU KARANTA: Sai dai kuyi hakuri amma bakuda hurumin gayyatar IGP - Falana ga Majalisa

Wasu dai na hasashen cewa Gwamnan na Ekiti Ayodele Fayose na son ya rufawa kansa asiri ne, shi ne yake yunkurin yin duk mai yiwuwa wajen ganin ya tabbatar da mataimakinsa a matsayin wanda zai gaje shi.

Fayose dai nada tsattsamar alaka da gwamnatin Najeriya kasancewar shi a jam’iyyar PDP mai adawa, ga shi baya iya shiru da bakinsa wajen sukar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Bayan faɗuwa zaben fidda gwani, wani ɗan takadar gwamna ya fice daga PDP

Bayan faɗuwa zaben fidda gwani, wani ɗan takadar gwamna ya fice daga PDP

Hukumar EFCC dai ita ma na da kwantacciyar magana tsakaninsu, ana kuma hasashen cewa da zarar ya sauka zasu kai masa goron gayyata kasancewar in ya saukan bashi da wata kariya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel