Wannan abin kunya har ina: An kama Uba da Dansa sun saci naira miliyan 2.4

Wannan abin kunya har ina: An kama Uba da Dansa sun saci naira miliyan 2.4

Ta tabbata a rayuwarnan wasu mutanen gaba suka baiwa abin kunya, inda a nan ma an kama wani Uba mai suna Femi Adelegan da Dancikinsa Daniel Adelegan da laifin satar kudi naira miliyan biyu da dubu dari hudu, mallakin wani Maigidansu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Femi mai shekaru 61 da Dansa Daniel mai shekaru 30, dukkaninsu mazauna unguwar Ori Oke, yankin Magodo dake jihar Legas sun gurfana a gaban wata Kotun majistri dake garin Ikeja, inda ake tuhumarsu da laifin hadin baki, da kuma aikata sata.

KU KARANTA: Boko Haram: An kashe Maciji ba’a sare kansa ba – Inji Majalisar dinkin Duniya

Dansanda mai shigar d akara, Sufeta Raphael Donny ya bayyana ma Kotu cewa Uba da Dan sun aikata laifin ne a tsakanin watan Agusta na shekarar 2015 da watan Oktoba na shekarar 2017, a kamfanin Deva Access and Empowerment International Ltd, inda suke aiki a matsayin jami’ai masu bada bashin kudi.

Wannan abin kunya har ina: An kama Uba da Dansa sun saci naira miliyan 2.4

Gudumar Kotu

“Bayan da kamfanin ta gudanar da bincike kudadenta, sai ta gani an batar da kudi naira miliyan 2.4, daga nan ta kai kara ga Yansanda, inda Yansandan suka kama wadanda ake zargi, su kuma suka tabbatar ma Yansandan cewa su suka saci kudin.” Inji Sufeta Donny.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito wadanda ake tuhumar sun musanta zarge zargen, inda bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkali mai shari’a A.O Adeboye ta bada belin kowannensu akan kudi naira dubu dari biyar tare da mutane biyu da zasu tsaya musu akan kudi N500,000.

Daga nan kuma mai shari’a ta dage cigaba da sauraron kara har sai ranar 22 ga watan Mayu na shekarar 2018.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel