Wani jigo a jami'iyyar PDP ya rasa dan sa

Wani jigo a jami'iyyar PDP ya rasa dan sa

Mun samu rahoton rasuwar Dipo, dan jigo a jam'iyyar PDP, Bode George. Ya rasu ne bayan da dade yana fama da wata rashin lafiya kamar yadda jaridar Cable ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng mu bata bayar da cikakken bayani akan rashin lafiyarsa ba amma an ce ya dade yana fama da ciwon kafin ya rasu a yau Alhamis.

Wani daga cikin iyalan Bode Goerge ne ya tabbatar da labarin rasuwar amma ya bukaci a sakaya sunansa saboda a halin yanzu ba'a bashi izinin zantawa da manema labarai ba.

Dan Bode George ya rasu

Dan Bode George ya rasu

A lokacin rayuwarsa, Dipo ya kasance baya shiga mutane da yawa hakan yasa ba'a san abubuwa sosai game da rayursa ba amma matar tsohon Sojin ruwa mai murabus, Feyi ce ta haife shi.

Bode George ya yi gwamna a jihar Ogun zamanin mulkin soja kuma daga bisani ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na yankin Kudu maso yamma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel