An kori wani babban alkalin gwamnatin tarayya daga aiki, an fara binciken wasu 7

An kori wani babban alkalin gwamnatin tarayya daga aiki, an fara binciken wasu 7

Hukumar kula da bangaren shari’a na kasa (NJC) ta amince da sallamar wani alkalin kotun gwamnatin tarayya daga aiki tare da fara binciken wasu alkalan guda bakwai.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan wani taro da mambobin majlisar koli na hukumar suka gudanar a ranakun Talata da Laraba, a birnin tarayya, Abuja, kamar yadda kakakin ta, Soyinka Oye, ya sanar.

Hukumar ta amince da sallamar mai shari’a Michael Goji na babbar kotun tarayya dake jihar Adamawa saboda ya ki amincewa ya koma wurin sabon aikin da aka mayar das hi a Mubi tun watan Yuli, 2017.

An kori wani babban alkalin gwamnatin tarayya daga aiki, an fara binciken wasu 7

An kori wani babban alkalin gwamnatin tarayya daga aiki, an fara binciken wasu 7

Kazalika hukmar ta amince da nadin wasu sabbin alkalai 22 da zasu rike ofisoshi daban-daban.

Gwamnan jihar Adamawa ne ya amince da bukatar sallamar mai shari Goji daga bakin aiki bayan hukumar kula da bangaren shari’a ta gabatar masa da rahoton wasu badakaloli da alkalin keda hannu a ciki.

DUBA WANNAN: Malamin da ya jawo aka datse hannun karamin yaro ya fuskanci fushin kuliya

Hukumar ta bukaci alkalin ya dawo da dukkan albashin da ya karba daga watan Yuli, 2017 zuwa yanzu tare da bayar da umarni ga gwamnatin jihar Adamawa ta zaftare adadin albashin daga kudin sa na ritaya idan bai mayar das u ba har zuwa lokacin.

Kazalika majalisar koli ta hukumar tayi watsi da wasu korafe-korafe a kan wasu alkalai da suka hada da; mai shari’a Paul Adamu Galinje, Aminu Sabo Ringim; alkalin alkalan jihar Jigawa, da Jastis Peter Umeadi; alkalin alkalai na jihar Enugu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel