Zambar N650m: Kotu ta kekashe akan bukatar Otiti ta ficewa daga Najeriya

Zambar N650m: Kotu ta kekashe akan bukatar Otiti ta ficewa daga Najeriya

A ranar Litinin din da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya dake jihar Legas, ta hau kujerar naki inda ta yi watsi da roko gami da koken wata jigo ta jam'iyyar PDP, Misis Olanrewaju Otiti dake neman ficewa daga Najeriya wajen neman lafiyar ta.

Otiti ta bayyana wannan bukata ne ga kotun da sanadin lauyan ta Akinola Oladeji, inda take nema samun dama ta ficewa daga kasar domin lafiyar ta sakamakon ciwon koda da take fama.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, kotun ta kekashe akan rashin biyan bukatar Otiti a bisa zargin ta da laifin zamba har ta Naira Miliyan 650 da tayi tarayya da da tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison Madukwe wajen aikatawa tare da wasu tsaffin shugabanni biyu.

Zambar N650m: Kotu ta kekashe akan bukatar Otiti ta ficewa daga Najeriya

Zambar N650m: Kotu ta kekashe akan bukatar Otiti ta ficewa daga Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu tuni kotun ta karbe fasfo din Otiti wanda zai ba ta damar ficewa daga kasar nan.

KARANTA KUMA: Shugabannin Najeriya sun jajintawa Rasuwar Sheikh Isyaka Rabi'u

A yayin gudanar da shari'ar, Alkali Muslim Hassan ya bayyana cewa, a sakamakon gazawar Otiti na bayar da gamsashen dalili ga kotu da ka iya zama hujjar ta na cewa ba za a iya duban lafiyar ta a kasar nan ba ya sanya ya yanke wannan hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel