Hukumar ‘Yan Sanda ta kai majalisa kara kotu akan kiran da ta yiwa IG, ta kuma bayar da dalilan da zasu hana a kara kiransa

Hukumar ‘Yan Sanda ta kai majalisa kara kotu akan kiran da ta yiwa IG, ta kuma bayar da dalilan da zasu hana a kara kiransa

- Hukumar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta kai majalisa kara kotu

- Shugaban hukumar ta ‘Yan Sanda yaki martaba kiran da majalisa tayi masa game da yanda ake kula da Sanata Melaye wanda ke hannunsu

- Hukumar ‘Yan Sandan tace Sanatocin suna daukar lamarin Sanata Melaye da muhimmanci kamar su aka tsare

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta kai majalisa kara kotu don sanin cewa idan ya dace a dokar kasa ace koda yaushe shugaban hukumar sai ya tsaya da kansa a gaban majalisa duk lokacin da majalisar ta kira shi.

Hukumar ‘Yan Sandan tace majalisar bazata kara kiran shugaban hukumar ba, har sai kotu ta yanke hukunci akan hakan.

David Igbodo, kwamishinan ‘Yan Sanda na bangaren ayyukan helikwatar hukumar ne ya bayyana haka a wani shiri na Sunrise Daily, shirin gidan Talabijin na Channels.

Hukumar ‘Yan Sanda ta kai majalisa kara kotu akan kiran da ta yiwa IG, ta kuma bayar da dalilan da zasu hana a kara kiransa

Hukumar ‘Yan Sanda ta kai majalisa kara kotu akan kiran da ta yiwa IG, ta kuma bayar da dalilan da zasu hana a kara kiransa

Hukumar ‘Yan Sandan ta mayar da murtanin ne game da furucin majalisar na cewa shugaban hukumar ta ‘Yan Sanda makiyin mulkin farar hula ne kuma bai cancanci rike wani matsayi ban a gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: An gano maganin Sanko

Bayan haka Legit.ng ta ruwaito cewa Ibrahim Idris, ya mayarwa majalisar da murtani game da furunta akansa, inda ya bayyana ta bakin mai magana da yawun hukumar ‘Yan Sandan, Jimoh Moshood, a ranar Laraba, 9 ga watan Mayu, ya zargi majalisar da bata masa suna, inda yace ya tafi wani muhimmin aiki ne lokacin da majalisar ta kirashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel