PDP tayi Allah wadai da Sufeto Janar na yan sanda bisa akan kin amsa gayyatar majalisa

PDP tayi Allah wadai da Sufeto Janar na yan sanda bisa akan kin amsa gayyatar majalisa

- Jam’iyyar PDP bayyana rashin jin dadinta game da yanda shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris, yaki amsa gayyatar da da majalisa tayi masa lokuta da dama

- An tsammaci Idris ya bayyana a gaban majalisar a Talata, amma yaki yaje, wanda wannan shine karo na uku kenan da majalisar ta gayyace shi amma yaki ya bayyana a gabanta

- Majalisar bisa ga irin wannan halayya da ya nuna ta jefa kuri’ar rashin tabbaci ga IGP, sannan kuma ta bayyana cewa bai cancanci rike wani matsayi ban a gwamnati

Jam’iyyar PDP bayyana rashin jin dadinta game da yanda shugaban hukumar ‘Yan Sanda Ibrahim Idris, yaki amsa gayyatar da da majalisa tayi masa lokuta da dama.

NAN ta ruwaito cewa majalisar ta tsammaci Idris ya bayyana a gaban majalisar a Talata, amma yaki yaje, wanda wannan shine karo na uku kenan da majalisar ta gayyace shi amma yaki ya bayyana a gabanta.

Majalisar bisa ga irin wannan halayya da ya nuna ta jefa kuri’ar rashin tabbaci ga IGP, sannan kuma ta bayyana cewa bai cancanci rike wani matsayi ban a gwamnati.

PDP tayi Allah wadai da Sufeto Janar na yan sanda bisa akan kin amsa gayyatar majalisa

PDP tayi Allah wadai da Sufeto Janar na yan sanda bisa akan kin amsa gayyatar majalisa

Sakamakon jin haka PDP tace abun da IGP yayi ba daidai bane, da yak i amsa gayyatar da majalisar tayi masa, don yayi asarar damar neman shawara daga majalisar game da hanyoyin da za’a bi don magance matsalolin rashin tsaro dake damun kasar.

KU KARANTA KUMA: Babu kaskantattu kamar masu yunkurin kawo sauyi a Kur'ani - Shugaban kasar Turkiyya

PDP ta bukaci shugaban majalisar Bukola Saraki da sauran Sanatoci dasu kare martabar majalisar da siyasar kasar baki daya, ba wai su tsaya a cewa Idris bai cancanci rike wani matsayi na gwamnati ba.

Idan dai bazaku manta ba hakan shine karo na uku da sufto janar na yan sandan ke kin amsa gayattar majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel