Saraki, Dogara suna goyon bayan Oshiomhole a matsayin dan takarar ciyaman na jam’iyyar APC

Saraki, Dogara suna goyon bayan Oshiomhole a matsayin dan takarar ciyaman na jam’iyyar APC

- Tsohon gwamnan jihar Edo a ranar Laraba ya bayyana cewa zai bayyana manufarsa ta neman kujerar ciyaman na jam’iyyar APC a ranar Alhamis

- Ya bayyana a garin Benin cewa shugaban Majalisa Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara zasu halarci taron tare da manyan mambobin jam’iyyar a ranar

- Oshiomhole yace gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha zai jagoranci gwamnonin jam’iyyar ta APC zuwa wurin taron wanda za’a gudanar a TRANSCORP Hilton

NAN daga garin Benin, ta ruwaito a ranar 9 ga watan Mayu, cewa Tsohon gwamnan jihar Edo a ranar Laraba ya bayyana cewa zai bayyana manufarsa ta neman kujerar ciyaman na jam’iyyar APC a ranar Alhamis.

Ya bayyana a garin Benin cewa shugaban Majalisa Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara zasu halarci taron tare da manyan mambobin jam’iyyar a ranar bikin bayyana manufar tasa ta tsayawa takarar kujerar ciyaman a jam’iyyar tasu.

Saraki, Dogara sun goyon bayan Oshiomhole a matsayin dan takarar ciyaman na jam’iyyar APC

Saraki, Dogara sun goyon bayan Oshiomhole a matsayin dan takarar ciyaman na jam’iyyar APC

Oshiomhole yace gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha zai jagoranci gwamnonin jam’iyyar ta APC zuwa wurin taron wanda za’a gudanar a TRANSCORP Hilton.

Tsohon gwamnan zai maye gurbin wanda zai sauka daga kujerar ta ciyaman a jam’iyyar Chief John Odigie-Oyegun, bayan ya samu amincewar shugaba Buhari.

Oshiomhole yace zai shiga cikin masu neman kujerar ne domin ya tallafa wurin cigaban jam’iyyar, shiyasa yace yanaso ya sanar da mambobin jam’iyyar da kuma mutanen Najeriya manufar tasa.

A halin da ake ciki, mambobin sabuwar PDP wadanda suka koma APC suka kuma taimakawa jam’iyyar taci zabe a shekarar 2015, sun bayyana rashin godiya da shugaba Buhari yake nuna masu da jam’iyyar, duk da kokarin da sukeyi masu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel