Fito na fito da Buhari: Tsohon gwamna yayi murabus daga kujeran da gwamnatin APC ta nada shi

Fito na fito da Buhari: Tsohon gwamna yayi murabus daga kujeran da gwamnatin APC ta nada shi

Tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola, ya yi murabus daga matsayin shugaban hukumar katin zama dan kasa wato National Identity Management Commission (NIMC).

Ya turawa shugaba Buhari wannan wasika ne a jiya Laraba, 9 ga watan Mayu, 2019.

Wasikar tace: “Ina mai rubuta takardar murabus a matsayin shugaban hukumar gane yan kasa wato National Identity Management Commission (NIMC) daga yau 9 ga watan Mayu 2018.”

“Na yi iyakan kokarina a wannan aiki kuma zan so in cigaba amma na samu wani harkar siyasa mafi muhimmanci kuma sabuwa wanda zai sa cigaba da wannan aiki zai mini wuya.”

“A matsayinka na daya daga cikin shugabanni na a gidan Soja, ina da tabbacin cewa zaka fahimci dalilina bisa harkan siyasan da nakeyi. A horon da na samu a gidan soja, an haramta min wani abu da zai nuna rashin biyayya.”

“Ina mai mika godiya bisa wannan daman da ka bani da kuma yarda da ni.”

Gabanin yanzu, jama’an jam’iyyar APC sun hurawa Oyinlola wuta cewa tun da ya fara nnua adawa da shugaba Buhari, to ya ajiye kujeran da shugaban ya basa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel