Babu kaskantattu kamar masu yunkurin kawo sauyi a Kur'ani - Shugaban kasar Turkiyya

Babu kaskantattu kamar masu yunkurin kawo sauyi a Kur'ani - Shugaban kasar Turkiyya

Shugaban kasar Turkiyya Erdoğan yayi Allah wadai da maguzawan Faransawa 300 bayan sun bukaci a cire dukannin ayoyin da ke sukar Yahudawa da Kiristoci daga Kur'ani mai mai girma.

Shugaban ya yi jawabi a taron da 'yan jam'iyyar AKP suka shirya a cibiyar babbar majalisar dokokin kasar Turkiyya, inda ya soki lamarin da kakkausar murya, ya kuma kalubalanci Faransawan wadanda a cikin su har da tsohon shugaba kasa,Nicolas Sarkozy.

Yace: "Wasu kaskantattu marasa kwakwale a Faransa sun fitar da wata sanarwa don nuna bukatarsu ta share dukannin wasu ayoyin Kur'anin da ke suka Yahudawa da Kiristoci.

Babu kaskantattu kamar masu yunkurin kawo sauyi a Kur'ani - Shugaban kasar Turkiyya

Babu kaskantattu kamar masu yunkurin kawo sauyi a Kur'ani - Shugaban kasar Turkiyya

“Shin sun taba karanta tsarkakkun litattafansu,Injila, Taurat, da kuma Zabura ko sau daya ? In sun taba karanta su,to za su so a yi musu kwaskwarima?".

KU KARANTA KUMA: Yakasai, Mantu, da kuma wasu shugabanin arewa sun gana da Saraki akan zaben 2019

“Shin ko ku waye ne da zaku taba abu mafi tsarki a addininmu? Ba zamu taba tsarkakkun litattafanku ba don kun yatsa ga namu,amma ku sani cewa, zamu yi nasara a kanku.Babu makawa,kun nuna mana yadda kuka kasance wulakantattu".

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel