Sojoji sun kashe wani tsohon soja, sun jefar da gawar sa

Sojoji sun kashe wani tsohon soja, sun jefar da gawar sa

Wasu sojoji dake aiki da wani kamfanin gine-gine a karamar hukumar Ahoada ta Gabas dake jihar Ribas sun azabtar da wani tsohon soja, Victor Ochoma, har sai da ya mutu.

Jaridar Punch ta rawaito cewar tsohon sojan, Victor, mai shekaru 25 ya bar aikin soja ne a 2014 bayan an saka shi cikin rubduna ta musamman da za a tura Maiduguri domin yaki da Boko Haram.

Rahotonni sun bayyana cewar, Victor, ya bar aikin soja ne saboda rashin ingantattun makaman da dakarun soji zasu yaki Boko Haram.

Sojoji sun kashe wani tsohon soja, sun jefar da gawar sa

Shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Yusif Buratai

Bayan ya bar aikin soja ne sai kamfanin gine-ginen da gwamnatin jihar Ribas ta bawa kwangilar gina hanyar da ta hada garuruwan Ahoada, Odiemerenyi, Adike, da Ihugbogo suka dauke shi aiki a matsayin maigadi. Kazalika an kara tura wasu sojoji domin tsaron ga ma’aikatan kamfanin.

Sojojin sun yiwa Victor dukan day a wuce kima ne bayan an kama wani mutum da laifin satar rodin kamfanin kuma ya bayyana cewar daya daga cikin masu gadi ne a wurin ya sayar masa.

DUBA WANNAN: An jefe wata mata har lahira saboda ta auri Maza 11

Punch ta rawaito cewar sojojin sun garzaya da gawar Victor inda suka jibge ta sannan suka yi sauri suka dawo wurin aikin su.

Wani dan uwan sad a ya samu ganin gawar say a bayyana cewar jinni ya dinga fita daga baki da hancin Victor saboda azabtarwar da sojojin suka yi masa.

Hukumar soji da ta ‘yan sanda bat ace komai a kan lamarin bay a zuwa yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel