Mutane tara suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a Taraba – ‘Yan Sanda

Mutane tara suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a Taraba – ‘Yan Sanda

- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Taraba a ranar Laraba ta tabbatar da mutuwar mutane tara a harin da akak kai a jihar a safiyar ranar a kauyen Tutuwa

- Jami’in hukumar ‘Yan Sandan mai kula da harkokin jama’a David Misal, yace wasu ‘yan ta’adda ne suka gudanar da wannan aika aika wadanda ba’a san ko suwanene ba

- Misal yace Aliyu Tafida mataimakin kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP) na hukumar tare da wasu shuwagabannin tsaro sun garzaya domin su binciki lamarin

Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Taraba a ranar Laraba ta tabbatar da mutuwar mutane tara a harin da akak kai a jihar a safiyar ranar a kauyen Tutuwa dake karamar hukumar Ussa a jihar Taraba.

Jami’in hukumar ‘Yan Sandan mai kula da harkokin jama’a David Misal, ya bayyanawa manema labarai cewa wasu ‘yan ta’adda ne suka gudanar da wannan aika aika wadanda ba’a san ko suwanene ba.

Misal yace Aliyu Tafida mataimakin kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP) na hukumar tare da wasu shuwagabannin tsaro sun garzaya domin su binciki lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yakasai, Mantu, da kuma wasu shugabanin arewa sun gana da Saraki akan zaben 2019

Rimansikwe Karma ciyaman na karamar hukumar Ussa, lokacin da yake tabbatarwa manema labarai da aukuwar lamarin yace har mutane uku sun samu raunuka, sannan kuma yace ‘yan ta’addan sun zagaye kauyen ne da misalign karfe 5 na asuba lokacin da ‘yan garin ke zuwa bauta, sun addamar da harin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Atiku ya kai tallafi ga wadanda harin bam ya cika dasu a msallacin Mubi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel